APC ta tsaida ranar da zata tantance yan takarar Shugabancin kasa na jam iyyarta |
Jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa za ta tantance wadanda suka siya fom din takarar shugabancin kasa a ranakun Litinin da Talata
Wannan na zuwa ne bayan da jam'iyyar ta sanar da cewa za ta yi zaben fidda dan takarar shugabancin kasanta a ranakun 6 da 8 ga Yuni masu zuwa
A halin yanzu, jam'iyyar za ta tantance 'yan takara 23, 11 daga ciki ranar Litinin yayin da sauran 12 sai ranar Talata mai zuwa